An dai gudanar da horon ne a wani wurin da ake gine-gine mai nisan fiye da kilomita 140 daga birnin Monrovia, inda sabbin ma'aikatan fiye da 100 dake aiki a wani kamfanin kasar Sin da ke Liberia suka kara ilminsu a fannin rigakafin cututtuka masu yaduwa.
Rahotanni sun bayyana cewa tun isar tawagar likitocin kasar Sin kasar Liberia a ranar 15 ga watan Nuwanbar bara, sun gudanar da ayyukan jinya ga mutane da dama dake dauke da cutar Ebola, tare da tura wasu masanan kiwon lafiya wurare daban daban, don horar da likitocin kasar ayyukan rigakafin cututtuka masu yaduwa.
Ya zuwa yanzu, yawan sojoji, da 'yan sanda, da likitocin kasar ta Liberia dake wurare daban daban, da tawagar likitocin Sin ta horar ya kai fiye da mutum 1500, matakin da ya taimaka kwarai wajen inganta aikin tinkarar cututtuka masu yaduwa a kasar, wanda kuma kasar Liberian ta yi matukar maraba da shi. (Zainab)