Gwamnatin kasar Somaliya ta tabbatar da cewa, babu ko da mutum guda da ya kamu da cutar Ebola a kasar.
Ministan kiwon lafiya na kasar Ali Mohamed Mohamud wanda ya bayyana hakan ga manema labarai, ya kuma ce, akwai mutum guda da ake zaton ya kamu da cutar a garin Buulo Sharey da ke yankin lower Shabelle mai suna Abdulkadir Jinow Barow, amma bayan an gudanar da bincike, an tabbatar da cewa, mutumin ba shi da cutar Ebola, amma duk da haka an garzaya da shi da wadanda ya yi mu'amula da su zuwa Mogadishu, inda likitoci za su yi musu gwaje-gwaje a matsayin wani mataki na riga-kafi.
Don haka ministan ya ce, suka fito karara don tabbatar wa duniya cewa, babu cutar Ebola a kasar ta Somaliya. (Ibrahim)