in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fadada ayyukan bada jinya a cibiyar sa ido ga mutanen da suka kamu da cutar Ebola ta asibitin sada zumunta a tsakanin kasar Sin da kasar Saliyo
2015-01-07 10:31:46 cri
A jiya da safe ne, aka kai mutane 5 da suka kamu da cutar Ebola zuwa cibiyar sa ido kan mutanen da suka kamu da cutar Ebola ta asibitin sada zumunta a tsakanin kasar Sin da kasar Saliyo dake yankin birnin Freetown,babban birnin kasar. Wannan ya alamta cewa, an fadada aikin bada jinya a cibiyar tun bayan da tawagar likitocin Sin dake kasar Saliyo suka shafe fiye da tsawon rabin wata guda suna kokarin kimtsawa.

An ce, bayan da aka fadada aikin bada jinya a cibiyar, an samar da sabbin gadaje 78 wadanda ake iya yin amfani da su wajen gudanar da aikin sa ido da kuma ba da jinya, wannan zai taka muhimmiyar rawa wajen aikin yin rigakafi da yaki da cutar Ebola a kasar.

Ya zuwa ranar 5 ga watan Janairu na bana, an karbi mutane 593 a cibiyar sa ido kan mutanen da suka kamu da cutar Ebola ta asibitin sada zumunta a tsakanin kasar Sin da kasar Saliyo da aka sa ido akan su don tabbatar da cewa ko sun kamu da cutar ko a'a a, yayin da aka tabbatar da mutane 248 daga cikinsu da suka kamu da cutar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China