Babban bankin kasar Liberia zai dauki wasu sabbin matakan rage tasirin da cutar Ebola ta haifar, ga harkokin banki, da ma sauran sassa na tattalin arzikin kasar.
A cewar gwamnan bankin na CBL Mills Jones, a baya an yi hasashen mizanin karuwar tattalin arzikin kasar zai kai ga kaso 6.6 bisa dari cikin shekaru 3 masu zuwa, amma yaduwar wannan cuta ya sanya wannan hasashe sakkowa zuwa kaso 1 bisa dari kacal.
Game da matakan da aka shirya dauka kuwa, Mr. Jones ya ce, babban bankin kasar zai biya dukkanin basukan da makarantu masu zaman kansu suka ci daga bankuna, kasancewar irin wadannan makarantu sun dade a rufe, ta yadda ba kuma za su iya biyan bashin da ake bin su ba.
Har wa yau a cewar sa, babban bankin zai tsawaita wa'adin biyan bashin kananan bankunan kasar da shekaru 2, za a kuma rage kudin ruwa daga kaso 3 zuwa kaso 2 bisa dari.
Liberia dai ita ce kasar da cutar Ebola ta fi yi wa matukar barna, inda baya ga rasa rayukan jama'a, tasirin cutar ya shafi harkokin noma, da cinikayya da ilimi da sauran su. (Saminu)