in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Saliyo ta fadada matakan yaki da cutar Ebola a kasar
2015-01-09 10:17:38 cri

Kasar Saliyo ta yanke shawarar fadada matakan yakin da ta ke da cutar Ebola a kasar, a wani mataki na hana yaduwar cutar a dukkan fadin kasar, musamman yankunan da ke yammacin kasar, ciki har da Freetown, babban birnin kasar.

Shugaban cibiyar yaki da cutar Ebola ta kasar (CEO) Palo Conteh ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai na farko da cibiyar ta kira bayan bikin sabuwar shekara.

Ya ce, manufar shirin ita ce kara daukar matakan da kasar ta ke da kuma dorawa kan nasarorin da ta samu a kokarin da ta ke na ganin an kawar da cutar kwata-kwata daga kasar.

Ya kuma danganta nasarorin da ta samu kan jerin matakan da aka dauka, ciki har da yadda ake kara ilimantar da jama'a kan wannan cuta, inda aka kara gano mutane da ke dauke da wannan cuta wadanda daga bisani aka kawo su cibiyoyin kula da wadanda suka kamu da cutar baya ga wadanda ke kawo kansu don a yi musu magani.

Yanzu haka akwai sama da gadaje kwantar da marasa lafiya 800 a cibiyoyin ba da magani da kula da wadanda suka kamu da cutar a dukkan fadin kasar ta Saliyo, baya ga dakunan bincike 11 da motocin daukar marasa lafiya 100. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China