Rahotanni sun bayyana cewa, firaministan ya gudanar da ziyara a kasashen Kazakhstan da Serbia, inda aka cimma nasarori masu yawa, yayin ganawar firaministan na Sin da takwaransa na kasar Kazakhstan a karo na biyu. Baya ga hakan, Li Keqiang ya kuma halarci taron shuagabannin mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai karo na 13, da aka gudanar a kasar ta Kazakhstan, da kuma taron shugabannin kasar Sin da na kasashen gabashi da tsakiyar Turai, da ya gudana a kasar Serbia.
Kaza lika firaministan na Sin ya halarci taron shugabannin shirin samar da ci gaban hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen dake kewayen kogin Mekong, karo na biyar da aka gudanar a kasar Thailand. (Maryam)