A gun shawarwarin, Li Keqiang ya bayyana cewa, kasar Sin ta yabawa ga kasar Serbia game da ganawar da ta shirya tsakanin shugabannin Sin da kasashen tsakiya da gabashin nahiyar Turai. A ganin mahalartar ganawar na kasa da kasa, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen tsakiya da gabashin nahiyar Turai ya dace da bukatu da halin bunkasuwa da ake ciki a kasashen, kana ya dace da fata bai daya da moriyar kasashen yankin da jama'arsu, ya ce har ila yau ya taimakawa inganta dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Turai. Don haka kasar Sin tana son yin kokari tare da kasashen tsakiya da gabashin nahiyar Turai ciki har da kasar Serbia don ci gaba da sa kaimi ga inganta hadin gwiwar dake tsakaninsu da kuma dangantakar dake tsakaninsu, kana tana son ci gaba da gayyaci masu sa ido da kungiyar EU ta tura su halarci ganawar, ta yadda za a iya tabbatar da bude kofa da amincewa da bambanci kan hadin gwiwar dake tsakaninsu. (Zainab)