Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya ba da tabbacin cewar, kasarsa za ta kafa wani asusun saka jari wanda darajarsa za ta kai dalar Amurka biliyan 3 domin taimaka wa kasashen tsakiya da gabashin Turai
Li ya bayyana hakan ne a yayin wani taro karo na 3 tsakanin shugabannin Sin da kasashen tsakiya da gabashin Turai wanda aka yi a Serbia.
Alkawarin taimakon da kasar ta Sin ta dauka na taimakawa kasashen Turai ya biyo bayan shekaru biyu bayan da kasar ta Sin ta kafa wani asusun bashi na musamman na dalar Amurka biliyan 10, domin taimakawa ayyukan kananan kungiyoyi dake tsakiya da gabashin Turai.
A jawabinsa ga taron, firaminsta Li ya ce, Sin za ta kara bunkasa bashin tare da rage kudin nauyin bashin.
Li ya yi shelar cewar, za'a kaddamar da rukuni na biyu na asusun saka jari na ayyukan gama kai tsakanin Sin da kasashen tsakiya da gabashin Turai mai darajar dalar Amurka biliyan 1 domin habbaka bangarorin 2. (Suwaiba)