A yammacin jiya Alhamis 20 ga wata, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da wakilai na Sin da na kasashen waje a birnin Hangzhou tare da yin shawarwari a yayin da suke halartar babban taron yanar gizo ta internet na duniya karo na farko.
Firaminista Li ya bayyana cewa, taken taron a wannan karo shi ne "Mu'amala da juna, moriyar juna, da kuma kulawa da juna". Wannan ya bayyana bude kofa ga kasashen waje da yin hadin gwiwa da neman samun moriyar juna. Bayan shekaru 20 da aka bunkasa yanar gizo ta internet, Sin ta riga ta kasance wata kasa mai karfi a wannan fanni. Ba ma kawai tana da wata babbar kasuwa ba, har ma ta mallaki sabbin fasahohi da kayayyaki da hanyoyi da yawa, tare da samar da guraben ayyukan yi masu dimbin yawa, musamman ma ga matasa, daliban jami'o'i da dama sun cimma burinsu na samar da sabbin ayyukan yi.
Firaminista Li ya jaddada cewa, gwamnatin Sin tana dora muhimmanci sosai kan bunkasa yanar gizo ta internet, tare da ba da goyon bayanta yadda ya kamata. A bana, gwamnatin kasar ta kara karfin kyautata manufofi, lamarin da ya taimaka wajen kara samun kamfanonin yanar gizo sama da miliyan 10, wanda yawansu ya karu da kashi 60 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara, kuma mafi yawansu kananan kamfanoni ne, wadanda suke da alaka da yanar gizo ta internet da fasahar sadarwa da sauransu. Za a kara kafa manyan kayayyakin amfanin jama'a na yanar gizo, da kara yawan mutanen dake iya amfani da kamfuta da internet. Kuma za a ci gaba da sa kaimi ga bunkasa fasahar yanar gizo da hidimomi, da kyautata manufofi a wannan fanni, tare da sa kulawa ga yanar gizo bisa doka, da yaki da ayyukan keta dokoki ta hanyar amfani da yanar gizo. Sin na fatan yin mu'amala da hadin gwiwa da sauran kasashen duniya a fannin yanar gizo bisa ra'ayin bude kofa ga juna da girmamawa juna, da zummar samun moriyar da yanar gizo za ta kawo mana tare.(Fatima)