Da yake tsokaci game da hakan Li Keqiang ya bayyana cewa, kamata ya yi a kara yin hadin gwiwa a fannonin kiyaye tsaro, da tattalin arziki da kuma al'adu.
Ya ce abu na farko shi ne a tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin. Kuma kasar Sin ta tsaya tsayin daka, wajen kiyaye zaman lafiya da lumana, da bunkasuwa a yankin, tare da bin hanyar samun ci gaba cikin kyakkyawan yanayi. Kaza lika Sin na da burin ci gaba da yin hadin gwiwar kasa da kasa domin sa kaimi ga bukasar zaman lafiya da wadata a duniya.
Na biyu ya ce kamata ya yi a kirkiro sabbin fannoni daga matsayin hadin gwiwar dake tsakanin kasashen yankin. Kasancewar kasar Sin tana da fasahohi na gina ababen more rayuwa, da kwarewa kan kera na'urori, da samar da kayayyaki masu inganci, kuma Sin tana son yin hadin gwiwa a tsakaninta da sauran bangarorin kungiyar SCO, domin cimma moriyar juna da bunkasuwa tare. Haka zalika kasar Sin tana da burin hada kai tare da bangarori daban daban na kungiyar, domin sa kaimi ga samar da sauki a fannonin ciniki da zuba jari, da rage kariyar da ake sanyawa harkokin cinikayya, da zuba jari, da kara samar da izinin shiga kasuwanni.
Na uku Mr. Li ya ce ya dace a dora muhimmanci kan mu'amalar al'adu, da zamantakewar rayuwar jama'a, da sa kaimi ga kara gudanar da ayyuka, da samar da aikin yi. Kasar Sin tana da sha'awar kara yin hadin gwiwa tare da kasashen dake wannan kungiya a fannonin aikin gona, da kiyaye muhalli, da kiwon lafiya, da sa kaimi ga kafuwar tsarin hadin gwiwa a fannin samar da isashen hatsi, da samar da horo ga kasashe mambobin kungiyar a fannin ilimin da kiyaye muhalli, da kuma kafa tsarin hadin gwiwa kan rigakafin cututtuka masu yaduwa. (Zainab)