Mr. Li wanda ya bayyana hakan yayin ziyarar aiki da ya gudanar a lardin Zhejiang dake gabashin kasar ta Sin, ya bayyana muhimmancin daukar wannan mataki ne bisa la'akari da kalubalen raguwar bunkasar tattalin arzikin da ake fuskanta a yanzu haka.
Ya ce duk da wannan kalubale kasar Sin ta samu zarafin samar da ayyukan yi ga jama'a, an kuma dada kyautata ayyukan hukuma, ta hanyar karawa hukumomi a matakin farko ikon gudanarwa. Lamarin da a cewarsa, ya taimaka kwarai wajen bunkasa sabbin sana'o'i masu yawa.
Kaza lika Firaminsta Li, ya ja hankalin kamfanoni da masana'antun kasar da su zage damtse, wajen fadada harkokinsu zuwa sassan duniya baki daya, tare kuma da fidda sabbin samfurin kayayyaki masu nagarta kirar gida.
Daga nan sai ya jaddada muhimmancin tallafawa kanana da matsakaitan bankuna, da nufin inganta shirin bunkasa yankin tattalin arziki na kogin Yangtzi.
Bisa kididdigar baya bayan nan dai karuwar tattalin arzikin kasar Sin ta yi kasa zuwa kaso 7.3 a watanni 4 na karshen shekarar nan, sabanin kaso 7.5 da aka samu a watanni 4 na tsakiyar shekarar ta bana. Wannan ne kuma kaso mafi kankanta, da tattalin arzikin kasar ya kai tun bayan watanni 4 na farkon shekarar 2009.