in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta rasa damar halartar gasar cin kofin Afirka
2014-11-30 16:09:00 cri

Kungiyar kwallon kafar Super Eagles ta Najeriya, wadda ke rike da kambin gasar kwallon kafa ta nahiyar Afirka ta bara, ta gaza samun damar halartar gasar da za a buga a badi, bayan ya tashi wasan ta na karshe na share fagen buga gasar kunnen doki ita da kasar Afirka ta Kudu.

Kulaf din na Super Eagles dai ya tashi 2 da 2 a wasan da ya gudana da Afirka ta kudu a ranar Laraba da ta gabata. Duk kuwa da cewa ita kungiyar Afirka ta Kudu, tuni ta samu damar halartar gasar cin kofin na Afirka dake tafe a farkon shekarar 2015.

A dai wannan rana ne kuwa, kungiyar kasar Ghana ta lashe Togo da ci 3 da 1, lamarin da ya baiwa Ghanan cikakkiyar damar shiga a fafata da ita a gasar ta cin kofin Afirka.

Dan wasan Ghana Majeed Waris ne dai ya ci wa kasar sa kwallon farko a mintuna 24 da fara wasan. Sai kuma kwallo ta biyu daga Mubarak Wakaso mintuna kadan bayan kwallon farko.

Bayan hutun rabin lokaci ne kuma, dan wasan gaban kungiyar Togo Floyd Ayite ya farke kwallo daya, kafin kuma mukaddashin kyaftin din kungiyar ta Ghana Agyemang Badu ya jefa kwallo ta 3 a minti na 69 da taka leda. Haka kuma aka tashi wasan ci 3 da 1.

Duk dai da cewa a wannan karo fitattun 'yan wasan Ghana kamar Kyaftin din kungiyar Asamoah Gyan, da 'yan wasan tsakiya Kwadwo Asamoah, da Andre Ayew ba su buga wasan ba, kungiyar kasar Ghana ta sake lashe Togo, bayan wasan da ta samu nasara kan Togon na watan Satumbar da ya gabata, wanda kungiyoyin biyu suka tashi 3 da 2.

Yanzu dai Ghana ce ke saman rukunin E da maki 11, a wasanni 6 da ta buga.

Za dai a gudanar da gasar cin kofin nahiyar Afirka ne na badi a kasar Equatorial Guinea, daga ranar 17 ga watan Janairu zuwa ranar 8 ga watan Fabrairu. Kuma kungiyoyin kasashen da za su fafata a gasar sun hada da Algeria, Burkina Faso, Kamaru, Cape Verde, Congo Brazzaville, jamhuriyar Dimokuradiya Congo. Sai kuma Gabon, Ghana, Guinea, Cote d'Ivoire, Mali. Sauran su ne Senegal, Afirka ta Kudu, Tunisia, Zambia, gami da mai karbar bakuncin gasar wato Equatorial Guinea.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China