in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayern Munich ya daga a gasar Bundesliga, bayan da ya doke Dortmund da ci 2 da 1
2014-11-05 16:34:06 cri
Kulaf din Bayern Munich na kasar Jamus ya daga a teburin gasar Bundesliga, bayan da ya samu nasarar doke Dortmund da ci 2 da 1. Yayin da kuma kulaf din Wolfsburg ya lallasa Stuttgart da ci 4 da nema, a wasannin mako na 10 da aka buga a ranar Asabar.

Dan wasan Dortmund Marco Reus ne dai ya fara bude jefa kwallo cikin mintuna 31 da fara wasa. Sai dai bayan hutun rabin lokaci wasan ya canza, bayan da Robert Lewandowski ya farkewa Munich din kwallon da aka zura mata cikin minti na 72. Daga bisani kuma Arjen Robben ya kara kwallo ta biyu ta bugun daga kai sai mai tsaron gida ana daf da tashi daga wasan.

Nasarar da Bayern din dai ta samu a wannan wasa ya daga matsayin ta a teburin na Bundesliga zuwa na daya, yayin da ita kuma Dortmund ta fada matsayi na 17 bayan wasannin ranar Lahadi.

A wasan Wolfsburg da Stuttgart kuwa, Wolfsburg din ce ta samu nasarar zura kwallaye bibiyu a farko da zangon wasan na biyu, matakin da ya sanya Stuttgart kara kwasar rashin nasara a karo na 5 cikin gasar.

Wannan nasara da Wolfsburg ta samu dai ya daga matsayin ta zuwa ta biyu a teburin gasar, yayin da abokiyar karawar ta Stuttgart ta fada zuwa na matsayi na 15.

Sai kuma karawar da aka yi tsakanin Hamburg da Bayern Leverkusen, wasan da Hamburg din ta lashe da ci 1 mai ban haushi. Alkalin wasan dai ya yi ruwan katin gargadi har 9 ga 'yan wasan bangarorin biyu, a kuma irin wannan yanayi ne a minti na 26 dan wasan Leverkusen Bernd Leno, ya yiwa Marcell Janssen keta a kusa da raga, nan take kuma alkalin wasa ya bada bugun daga kai sai mai tsaron gida. Wanda hakan ne kuma ya bada damar jefa kwallo daya tilo da aka ci a wasan.

Da wannan nasara da Hamburg ta samu yanzu ta daga zuwa matsayi na 14, yayin da ita kuma Leverkusen ke matsayi na 5.

A wasan Bremen da Mainz kuwa, Bremen din ce ta doke abokiyar karawarta da ci 2 da 1. Dan wasan Bremen Franco Di Santo ne dai ya jefa kwallaye biyu a ragar Mainz daf da tafiya hutun rabin lokaci da kuma bayan dawowa daga hutun. Kafin hakan dai dan wasan gaban Mainz Shinji Okazaki ne ya bude zura kwallo daf da fara wasan.

Shi kuwa kulaf din Hannover ya samu nasara a karo na 5 ne da kwallo 1 tilo, bayan da dan wasan Frankfurt Alexander Madlung ya ci garin su, wanda hakan ya kara yawan rashin nasarar Frankfurt din zuwa wasanni 4.

Sauran wasannin da aka buga ranar Lahadi kuwa sun hada da Monchengladbach da Hoffenheim, wanda aka tashi Monchengladbach na da kwallo 3 Hoffenheim na da 1. Sai kuma Cologne wadda ta sha kashi hannun Freiburg da kwallo daya mai ban haushi. Haka kuma Paderborn ta lallasa Hertha Berlin da ci 3 da 1.

Sakamakon wasannin karshen makon dai ya nuna yadda Bayern Munich da Wolfsburg da Monchengladbach suka dare matsayi na 1 da na 2 da na uku a saman teburin na Bundesliga. A can kasa kuwa akwai Freiburg da Dortmund da kuma Wender Bremen a matsayi na 16 da 17 da 18.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China