Jaridar Tehran Times ta kasar Iran ta fidda hakan a Lahadin da ta gabata, tana mai rawaito shugaban hukumar wasan kwallon kafar kasar ta Iran, mista Ali Kaffashian, na cewa, hukumar wasan kwallon kafar Kenya ta nemi kasar Iran din ta biya ta dalar Amurka 50,000, da kuma kudin sayen tikitin jirgin sama ga 'yan tawagar ta kafin ta amince ta halarci wasan na sada zumunci. Dangane da hakan, shugaban ya ce wannan ba bukata ce da ta dace da Kenya dake matsayi na 116 a duniya ta gabatar ba. Hakan dai na nufin Kenya ta zura jiki game da wannan bukata da Kenya ta bayyana.
Da ma dai kungiyar Iran din na da shirin buga wasu wasanni na sada zumunta, domin share fagen babbar gasar cin kofin nahiyar Asiya na shekarar 2015 dake tafe. Kungiyar dai wadda Carlos Quieroz ke horaswa za ta fafata ne da kungiyoyin kasashen hadaddiyar daular Larabawa, da Qatar, da Bahrain a rukuni na 3 na waccan gasa dake tafe tsakanin ranar 9 zuwa 31 ga watan janairun badi a kasar Australia.
Yanzu haka dai Iran din na neman wata kungiya ta daban daga nahiyar Afirka, wadda za ta maye gurbin kungiyar kasar Kenya a wasan na sada zumunci da take fatan bugawa a ranar 14 ga wata. Haka zalika kungiyar na da shirin karawa da Koriya ta Kudu a birnin Tehran, da kuma kungiyar kasar Iraki a birnin Sydney, kafin a fara gasar cin kofin nahiyar ta Asiya.