in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Messi ya sake kafa tarihin zura kwallaye
2014-11-27 10:19:53 cri
Leo Messi na kungiyar kwallon kafar Barcelona ya sake kafa sabon tarihi a fagen zura kwallaye a raga. Rahotanni dai sun bayyana Messi a matsayin dan wasan da ya fi kowa yawan kwallaye, a gasar ajin kwararru ta kasar Sifaniya, bayan da ya ci kwallaye 3 a wasan da Barcelona ta buga ranar Asabar da kulaf din Sevilla.

A wannan wasan ne dai Messi ya ci kwallon sa ta 252, da ta 253 da kuma ta 254, wanda hakan ya bashi damar dara tsohon dan wasan Athletic Bilbao Telmo Zarra a yawan kwallaye.

Duk dai da cewa Messi bai gana da manema labaru bayan wannan nasara da ya samu ba, sakamakon wasu kalamai da kafofin watsa labaru suka fitar dake nuna yadda ya bayyana rashin gamsuwa, da kasancewar sa a kulaf din na Barcelona, a daya hannun 'yan kallo kusan 100,000 da suka kalli wasan na ranar Asabar sun rika sowa suna kiran sunan sa.

Daga bisani kuma ya aike da wani sako ta shafin sa na facebook, wanda ke cewa "lokacin da na ci kwallon farko a gasar kulaflikan kasar Sifaniya, ban yi zaton zan iya wuce gwarzo Telmo Zarra ba, "Amma a yanzu da na cimma wannan buri, ina godiya ga daukacin wadanda suka taimaka min kaiwa ga wannan nasara. Na sadaukar da ita ga daukacin wadanda suka ba ni gudummawa, da ma wadanda a yanzu ba sa nan. Ina gode musu, kuma suna cikin rai na. Na gode, a kalaman Leonel Messi.

A wani ci gaban kuma shi ma kocin kulaf din na Barcelona Luis Enrique, ya karfafa kalaman masu yabon kwarzon dan wasan kungiyar ta sa, ya na mai cewa abu ne mai wuya a iya kwatanta wani dan wasa da Messi, kana kungiyar sa ta yi sa'ar samun damar amfanuwa daga basirar Messi. Kaza lika kocin na Barca ya ce wannan wata dama ce ta musamman da kungiyar sa ta samu wadda ke da wuyar maimaituwa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China