in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kulaf din Ajax ya maye gurbin PSV a saman teburin gasar Eredivisie
2014-11-27 10:21:32 cri
Kulaf din Ajax na kasar Holland ya doke takwaransa na Heerenveen da ci 4 da 1, a wasan da suka buga ranar Asabar, ya yin da kulaf din dake matsayi na daya a da wato PSV ya tashi nasa wasan kunnen doki 1 da 1 da Groningen a ranar Lahadi, wanda hakan ya sanya Ajax dagawa zuwa matsayi na daya a saman teburin, ya yin da PSV ya koma na biyu.

Kaza lika a wasannin ranar ta Asabar Feyenoord ya samu nasara kan FC Dordrecht da ci 2 da nema. Sai kuma Vitesse wadda ta sha kashi a hannun AZ Alkmaar da ci 1 da nema.

A ranar Lahadi kuwa, baya ga wasan PSV da Groningen, kulaf din FC Twente ya doke PEC Zwolle da ci 2 da 1.

Yanzu haka dai baya ga Ajax da PSV dake matsayi na daya da na biyu, akwai kuma Feyenoord da Vitesse dake matsayi na 3 da na hudu a teburin gasar ta Eredivisie. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China