in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cimma matsaya game da komawar shugaban NFF mukamin sa
2014-08-20 16:57:41 cri

Daukacin sassan masu ruwa da tsaki sun amince da kudurin komawar shugaban hukumar kwallon kafar Najeriya Aminu Maigari kan mukamin sa. Hakan a cewar ministan wasannin kasar Tammy Danagogo ya biyo bayan yardar da dukkanin sassan da batun ya shafa suka yi, na warware takaddamar da ta kai ga dakatar da Maigari daga mukamin nasa ne a ranar 24 ga watan Yulin da ya gabata, bayan da aka zarge shi da saba dokokin aiki.

Kafin kaiwa ga wannan sulhu dai sai da kwamitin zartarwar hukumar ta NFF ya nada mataimakin sa Mr. Mike Umeh ya maye gurbin sa. Matakin da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta nuna kin amincewa da shi. Inda daga bisani ta umarci NFFn da ta maida Maigari kan mukamin sa, tare da bashi damar jagorantar babban taron hukumar dake tafe ranar 26 ga watan nan na Agusta.

Cimma wannan matsaya a cewar ministan wasannin kasar ya kawo karshen cece-kuce da ake yi game da matsayin shugaban hukumar ta NFF, kana an kai ga warware dukkanin matsalolin da suka haifar da sa-in-sa a baya.

Bugu da kari Mr. Danagogo ya ce daukacin jami'an hukumar da na ma'aikatar wasanni sun amince su yi aiki tare da Maigari, domin tabbatar da nasarar zaben sabbin shuwagabannin hukumar na gaba.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China