in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bundesliga: Hamburg ta lashe wasan ta da Bremen, yayin da Stuttgart ta sha kashi hannun Augsburg
2014-11-27 10:20:44 cri
A ci gaba da buga gasar Bundes Liga ta kasar Jamus, kulaf din Hamburg ya lashe wasan da ya buga da Bremen Hamburg da ci biyu da nema, a wasan mako na 12 da ya gudana a ranar Lahadi.

'Dan wasan kulaf din na Hamburg Artjoms Rudnevs ne dai ya jefa kwallon farko a ragar Bremen a minti na 83 da take wasa, kafin daga bisani yunkurin da mai tsaron gidan Bremen Raphael Wolf ya yi na tare wata kwallon ya haifar da fadawar ta cikin raga, mintuna 3 cikin karin lokaci, haka kuma aka tashi Hamburg na da ci biyu Bremen na nema.

Wannan nasara dai da Hamburg ta samu ta bata damar fita daga jerin kulaflikan da ka iya fadowa daga wannan gasa, bayan da ta daga zuwa mataki na 15 a teburin, yayin da Bremen ta fada na 17.

A daya wasan da aka buga a wannan rana kuwa, Stuttgart ta sha kashi hannun Augsburg da ci 1 da nema. Wannan ne dai karo na 7 a jere, da Stuttgart ta rasa nasara a wasannin da take bugawa cikin wannan gasa. Kafin hakan kuwa sai da alkalin wasa ya kori Daniel Schwaab na Stuttgart daga filin wasan cikin minti na 24.

A kuma cikin minti na 72 ne Augsburg ta samu bugun daga kai sai mai tsaron gida, inda nan take Paul Verhaegh ya jefa kwallo a zaren Stuttgart.

Da haka kuma Augsburg ta samu damar matsawa zuwa matsayi na 6 a teburin na Bundesliga, yayin da abokiyar karawar ta Stuttgart ta fada matsayi na 18.

Bayan kammalar wasannin karshen makon jiyan dai Bayern München ce ke matsayi na 1 a tebir, sai kuma Wolfsburg a matsayi na 2, ya yin da Borussia Mönchengladbach da Beyern Leverkusen dake matsayi na 3 da na 4

A can kasan teburin kuwa, Borussia Dortmund ce ke matsayi na 16, sai

Werder Bremen ta 17, ya yin da Stuttgart ke matsayi na 18.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China