in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Evergrande ta sake lashe kambi a gasar Super League ta kasar Sin
2014-11-07 17:03:32 cri

Game da wasannin da suka gudana a nan kasar Sin, dazu nan an kawo karshen wata kakar wasa ta gasar Super League ta wasan kwallon kafa, inda Guangzhou Evergrande ta lashe kambi. Hakan ya zama karo na hudu a jere da kungiyar Evergrande ta lashe wannan kambi.

Evergrande ta kare kambin na ta ne biyan ta tashi kunnen doki da kungiyar Shandong Luneng da ci 1 da 1, a karshen wasan wannan kakar wasa da ta zo karshe a ranar Lahadi 2 ga watan nan. Da ma dai kungiyar ta Evergrande kunnen doki kadai take nema domin samun damar kare kambi na ta a wannan kakar wasa.

Kulaf din Evergrande dai ya taba lashe gasar zakarun nahiyar Asiya ta shekarar 2013, kungiyar ta kuma kasance ta farko a teburin Super League na kasar Sin, da maki 70 a wasanni 30, sama da kungiyar Beijing Guoan dake matsayi na 2 da maki 30.

A wasan na karshe kungiyar Luneng ce ta fara jefa kwallo a mintuna 12 da take wasa ta hannun Liu Binbin. Sai dai kafin tashi daga wasan Evergrande ya samu damar rama kwallon da aka zura masa cikin mintuna 43 na wasan ta hannun dan wasan kasar Brazil Elkeson. Bayan dawowa hutun rabin lokaci, Evergrande ta sake samun wasu damammaki, amma ta gaza jefa karin kwallaye cikin ragar abokiyar karawarta.

A wannan kakar wasa 'yan wasan Evergrande baki daya sun jefa kwallaye 76 cikin raga, ciki hadda kwallayen da Elkeson ya ciwa kungiyar guda 28.

Sai dai a nashi bangaren babban kocin kungiyar Marcello Lippi ya bayyana niyyarsa ta yin murabus bayan kawo karshen kakar ta bana, inda ya ce sakamakon yawaitar shekarun sa, ba ya fatan jagorantar kungiyar a kakar wasa dake tafe, don haka a cewar sa kulob din zai samu wani sabon koci a kakar wasan dake tafe.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China