in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Real Madrid ta zama kan gaba a teburin La Liga
2014-11-05 16:33:08 cri
Kwanaki 10 da fara wasanni a kakar wasa ta La Liga a kasar Sifaniya, kungiyar Real Madrid ta dare matsayi na farko a teburin gasar bayan ta lallasa kungiyar Granada da ci 4 da nema.

Wasan da aka buga a filin wasan Los Carmenes na kulob din Granada a ranar Asabar da ta wuce, ya baiwa Real Madrid din damar lashe wasa a karo na 11 a jere. Cristiano Ronaldo ne dai ya fara ciwa kungiyar sa kwallon farko, mintuna 2 bayan take wasan, kwallon da ta zama ta 17 da ya ci a wannan kakar wasanni.

Sai kuma kwallon da James Rodriguez ya zura cikin ragar kungiyar Granada mintuna 32 bayan fara wasan. Kwallon Benzema ita ce ta uku ga Madrid. Dan wasan dan kasar Faransa ya ci kwallon sa ne a wannan rana, wadda ta zame masa mai muhimmanci a ranar fitowarsa ta 250 a matsayin daya daga cikin 'yan wasan kungiyar ta Real Madrid. Har wa yau dan wasan Madrid din James ya sake ci wa kulaf din kwallo ta 4 ana daf da tashi daga wasan.

A nata bangare, kungiyar Barcelona ta ci karo da rashin nasarar farko a gida, bayan da Celta Vigo ta doke a wasan da suka tashi daya da nema a filin wasan Camp Nou a ranar Asabar.

Hakan dai ya biyo bayan nasarar da Real Madrid ta samu kan ta da ci 3 da 1 a makon da ya gabata.

Yanzu haka dai Valencia ce ke biyewa real Madrid a matsayi na biyu, sai kuma Atlentico Madrid da Barcelona dake matsayi na uku da na hudu.

Can kuwa a kasan teburin Real Socieded ce ke na 19 a matsayi na kusa na karshe, yayin da kuma Cordoba ke na karshe a matsayi na 20.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China