An dai buga wasan na karshe ne a filin wasan Mineirao dake birnin Belo Horizonte, inda Ricardo Goulart na Goias ya fara bude ragar Cruzeiro. Sai dai daga bisani, 'yan wasan Cruzeiro Samuel, da Everton Ribeiro sun ciwa kulaf din na su kwallaye daidaya, wanda hakan ya baiwa Cruzeiro damar lashe wasan, tare da kare kambinsa, duk da cewa akwai sauran wasanni 2 da suka rage ya buga.
Da yake tsokaci game da yanayin wasan dan wasan tsakiyar Cruzeiro Ribeiro, ya ce filin wasan bai da dadin taka leda, amma duk da haka sun kai ga cimma burin su na lashe wasan.
Wannan dai nasara ta sanya kulob din na Cruzeiro samun nasarar daukar wannan kofi har sau 4 a gasar ta Serie A ta kasar Brazil, jimillar da ta yi daidai da ta kulaflikan Vasco da Gama, da Fluminense, wadanda su ma kuloflika ne na birnin Rio.
Yanzu haka dai kulaflikan da suka dara Cruzeiro daukar wannan kofi su ne Flamengo, da Corinthians wadanda suka dauki kofin sau biyar-biyar, sai kuma Sao Paulo da ya dauka sau 6, da kuma kulaflikan Palmerias, da Santos wadanda suka dau kofin sau takwas-takwas.(Bello Wang)