in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iraq ta ki amincewa da kasashen waje su tura sojoji zuwa kasarta
2014-11-07 20:33:28 cri
Ministan harkokin wajen kasar Iraq Ibrahim al-Jaafari ya bayyana a ran 6 ga wata a babban birnin kasar Turkiya, Ankara cewa, kasarsa na maraba da goyon bayan da kasashen waje suke baiwa kasar kan harkar soja, da suka hada da kayayyakin sojoji da horaswar da suka baiwa sojojin kasar, amma kasar Iraq ba ta amince da kasashen ketare da su tura sojoji zuwa kasar ba.

A yayin taron kungiyar nazarin manyan tsare-tsaren kasa da kasa na Turkiya da aka yi a wannan rana, Ibrahim al-Jaafari ya bayyana cewa, jama'ar kasar Iraq ne kawai suke da ikon yaki a kasarsu da kansu.

Haka kuma, Ibrahim al-Jaafari ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su samar da karin taimakon jin kai ga 'yan gudun hijira na kasarsa wadanda a halin yanzu ke fama da hare-haren kungiyar IS, da kuma taimaka wa kasar wajen sake gina kanta. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China