Wannan jami'i ya bayyana cewa, sojojin tsaron kasar dake sansanin sun kaura zuwa sansanin al-Asad na yankin Bagadaza dake da nisan kilomita 40 daga arewa maso yammacin birnin Heet, tare da makamansu. Hukumar tsaron kasar ta bayar da labari cewa, an samu fashewar boma-bomai uku a birnin Baghdad, wadanda suka haddasa mutuwar mutane 17 baya ga mutane 60 da suka ji rauni.
Ministan harkokin wajen kasar Britaniya dake ziyara a kasar Iraki Philip Hammond da takwaran aikinsa na kasar Iraki Ibrahim al-Jaafari sun gudanar da taron manema labaru tare a ranar 13 ga wata, inda suka bayyana cewa, ba a iya canja yanayin yakin kasar Iraki ta hanyar kai hari ta sama kawai ba, kasar Britaniya da kasashe kawayenta za su taimakawa kasar Iraki wajen sake kafa da horar da sojoji, da samar da fasahohi da sauran gudummawa ga gwamnatin kasar Iraki. Kuma Al-Jaafari ya jaddada matsayin gwamnatin kasar Iraki na kin amincewa da sojojin kasa na kasashen waje su shiga kasar Iraki don yaki da dakarun kungiyar ISIS. (Zainab)