Wani jami'in 'yan sanda ya shaida wa 'yan jarida cewa, a daren nan a wani dan kunar bakin wake ya tada bom dake jikinsa a cikin masallacin 'yan darikar Shi'a dake yammacin birnin Baghdad a lokacin da ake gudanar da salla. Wanda ya sa mutumin da kuma sauran mutane 21 suka mutu nan da nan, yayin da wasu 25 suka ji rauni.
Jami'in 'yan sanda ya kara da cewa, harin ya lalata wasu gine-gine dake kewayen masallacin.
Tun daga farkon shekarar bara, ake samun hare-hare da rikice-rikice a kasar Iraki, lamarin da ya kara tsananta halin tsaro a wannan kasa. Bisa sanarwar da tawagar MDD mai bada taimako ga kasar Iraki da ofishin kula da harkokin kiyaye hakkin dan Adam suka gabatar, an ce, yawan mutanen da suka mutu a sakamakon tashe-tashen hanhalin da aka samu a kasar Iraki a farkon rabin shekarar bana ya kai 5576, kuma mutane fiye da dubu 11 ne suka ji rauni. (Zainab)