in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan wajen Nigeria ya bukaci a daina nuna banbanci tun da WHO ta wanke kasar daga Ebola
2014-10-23 14:14:32 cri

Ministan harkokin waje na tarayyar Nigeria Aminu Bashir Wali, ya yi kira a kan kasashen duniya da su dakatar da duk wani nuna banbanci a kan 'yan Nigeria, musamman saboda hukumar lafiya ta duniya WHO ta rigaya ta wanke Nigeria daga cutar Ebola.

A ranar Litinin da ta wuce ne hukumar lafiya ta duniya ta wanke Nigeria daga cutar ta Ebola bayan an kasa samun wasu sabbin mutane dake dauke da cutar ta Ebola bayan kwanaki 42.

Wata sanarwa daga ofishin ministan harkokin wajen kasar ta ce, tun da Nigeria ta samu nasarar dakile cutar ta Ebola, babu kuma wani dalilin da zai sa a nunawa 'yan Nigeria banbanaci ko tsangwama a yayin da suke gudanar da tafiye-tafiyensu a duk fadin duniya.

Sanarwar ta ce, hukumar lafiyar ta duniya ta yanke hukuncin ne na cewar, babu cutar Ebola a Nigeria bayan da aka yi kwanaki 21 ba'a samu wani sabon mutum ba da ya kamu da cutar, kuma bayan nan aka kara wasu kwanuka 21, jimla kwanuka 42 nan ma ba'a samu kowa dauke da cutar ta Ebola ba.

Sanarwar ma'aikatar harkokin wajen Nigeriyar ta ce, wannan nasara ta nuna kokarin da shugaban kasar Goodluck Jonathan ke yi a wajen murkushe cutar a Nigeria.

Sanarwar ta yaba da tallafi da matakan da hukumar lafiya ta dauka wajen dakile yaduwar cutar a Nigeria. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China