Wani babban jami'i MDD ya kara nanata cewar, MDD a shirye take ta marawa kasar Ghana baya a kokarin da take yi na dakile yaduwar Ebola.
A yayin da yake jawabi a birnin Accra a lokacin bukin cika shekaru 69 na ranar MDD, jami'in MDD a kasar Ghana Wolfgang Haas ya ce, MDD tana da wani babban nauyi na daukar matakai a cikin gaggawa domin dakile yaduwar Ebola.
A Haas ya kara da cewar, MDD tana aiki kafada da kafada da gwamnatin Ghana domin tabbatar da cewar, kasar ta Ghana ta mallaki dukanin tanade-tanaden da ake bukata da kayan aiki da ma'aikata domin kare jama'ar kasar daga yaduwar cutar Ebola.
Taken bukin ranar MDD na wannan shekarar shi ne "zamantowa 'dan kowace kasa da matasa", kuma taken bukin ranar MDD a kasar ta Ghana shi ne "hada kawunan matasa da ci gaban kasa."
Mataimakin ministan harkokin waje da hadin kan yankunan kasar ta Ghana Kwesi Quartey ya yi kira a kan matasa da su amshi kalubale domin samar da kafofi na bunkasa ci gabansu. (Suwaiba)