Magatakardan MDD Ban Ki-moon ya yi maraba da karin taimakon kudade da ake samu da kuma na kayayyakin aiki daga kasashen duniya, domin taimakawa wasu kasashen Afrika ta yamma yaki da barkewar cutar Ebola.
Wata sanarwa wacce kakakin magatakardan MDD Stephane Dujarric, ya rabawa manema labarai ta ce, Ban Ki-moon ya jaddada cewar, matsalar cutar Ebola matsala ce da ta shafi daukacin duniya, wacce kuma ke bukatar dimbin taimakon gaggawa daga kasashen duniya.
Sanarwar ta kara da cewar, magatakardan MDD ya mika godiyarsa ga gwamnatocin Australia, Columbia da Venezuela, saboda taimakon kudade da suka bayar wanda ya kai adadin dalar Amurka miliyan 14, da kuma alkawurra da suka gabatar ga asusun gidauniyar taimakon kasashen dake fama da cutar Ebola, sanarwar ta ce, a jiya Talata ita ma kasar Korea ta Arewa ta dauki alkawarin bayar da dalar Amurka miliyan biyar ga asusun gidauniyar taimakon.
Kawo ya zuwa Litinin, alkalumma sun nuna cewar, asusun taimakawa kasashen dake fama da Ebola wanda magatakardan MDD Ban Ki-moon ya kaddamar domin daukar mataki na dakile bazuwar cutar Ebola yana da adadin kudade da suka haura dalar Amurka miliyan 8.8 a banki da kuma wasu kudade dalar Amurka miliyan 5, wanda aka yi alkawarin za'a baiwa asusun agajin na Ebola.
Ga baki daya dai an yi alkawari za'a bayar da taimako na fiye da dalar Amurka miliyan 43.5, wannan ya sa magatakardan MDD ya gabatar da roko ga kasashen duniya, da su tabbata cewa, sun cika alkawurran da suka dauka na bayar da taimakon kudade domin yaki da cutar ta Ebola mai saurin kashe jama'a. (Suwaiba)