Kasashe takwas na kungiyar tattalin arziki da kudi ta yammacin Afrika (UEMOA) sun dauki niyyar fitar da dalar Amurka miliyan 1,5 domin tallafawa kasashen Guinea, Saliyo da Liberiya da suka fi fama da cutar Ebola, a cewar wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar a ranar Litinin a birnin Ouagadougou na kasar Burkina-Faso, inda shugabannin wadannan kasashe suka yi taro domin bikin cikon shekaru ashirin da kafa kungiyar, shugabannin kasashen kungiyar UEMOA, na nuna damuwa sosai da halin da ake ciki a shiyyar yammacin Afrika dalilin annobar cutar Ebola, suna bayyana goyon bayansu ga kasashen da matsalar ta shafa da al'ummominsu, in ji sanarwar.
Kasar Senegal, da ta kasance kasa guda dake cikin kungiyar UEMOA da ta samu mutum guda da cutar Ebola, ta kai ga cimma nasarar killace annobar ta hanyar ba da kulawa cikin nasara ga wannan maras lafiya, a yayin da tuni cutar Ebola ta kashe mutane fiye da dubu hudu, kana da mutane fiye da dubu tara da dari biyar da suka kamu da cutar tun lokacin barkewarta a farkon shekara a kasar Guinea, Liberiya da Saliyo. Shugabannin kungiyar UEMOA sun yi maraba da kokarin gamayyar kasa da kasa wajen yaki da wannan cuta, haka kuma sun bukaci da a cigaba da ba da hadin kai yadda ya kamata domin dakatar da yaduwar cutar Ebola da kuma bullo da magani ko allurarta cikin gaggawa, ta yadda za'a samu damar kawar da wannan cuta daga doron kasa. (Maman Ada)