Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Saliyo suka bayar a ranar 22 ga wata, an ce, jama'a dake birnin Koidu na kasar da masu ba da jinya kan cutar Ebola sun ta da rikici a tsakaninsu a ranar 21 ga wata, wanda ya haddasa mutuwar mutane biyu.
Labarin ya ce, dalilin da ya sa abkuwar rikicin shi ne sabo da wani mutum ya ki amincewa da likitoci su dauki mahaifiyarsa da ake zaton kamuwa da cutar Ebola. Sai dai ya bukaci likitoci da su yi binciken jinin mahaifiyarsa a cikin gidansa, wanda ya haddasa rashin gamsuwar 'yan sanda da suka zo tare da likitocin. A yayin rikicin, 'yan sanda sun yi mafani da bindigogi, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane biyu. Daga baya kuma lamarin ya tsananta a lokacin da jama'a suka yi wa wannan tawaga taron dangi.
Bangaren 'yan sanda na kasar Saliyo ya bayyana cewa, Wasu ababen more rayuwa da dakunan kwana sun lalata sakamakon rikicin, har ma wani gidan rediyo dake birnin Koidu ya rushe. An kafa dokar hana fitar dare a birnin, kuma kura ta lafa a yanzu. (Zainab)