Shugaban tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan ya yi kira da a kara matsa lamba wajen yaki da cutar Ebola, a yayin da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa, a yanzu kasar ba ta da cutar Ebola. A yayin da yake mai da martani kan wannan sanarwa, shugaban Najeriya ya mika wannan takardar shaida ga kwazon ma'aikatan kiwon lafiya, ma'aikatan sa kai da al'ummar Najeiya masu kishin kasa da suka taimakawa gwamnati wajen samun nasara kan wannan cuta. Wakilin kungiyar WHO a Najeriya, Rui Gama Vaz, ya mika wannan takardar shaida ga hukumomin kasar a ranar Litinin a birnin Abuja, bayan makwanni shida ba tare an gano wani sabon mutum da ya kamu da cutar ba a wannan kasa dake yammacin Afrika.
Mista Jonathan ya bayyana cewa, nasarar da Najeriya ta samu wajen yaki da cutar Ebola ya samu yabo daga kasa da kasa, kuma ya nuna cewa, 'yan Najeriya suna iyar kai ga cimma nasara idan suka mai da bambance bambancensu gefe guda, kana su yi aiki tare. Shugaba Goodluck Jonathan ya yi kira ga 'yan Najeriya da su tsaya cikin shirin ko ta kwana domin hana sake shigo da cutar a cikin kasar. (Maman Ada)