Kakakin magatakardan MDD Stephane Dujarric ya ce, MDD na jagorantar wani kokari da kasashen duniya ke yi na aikewa da kayayyakin aiki da kuma taimakon agaji zuwa kasashen Afrika ta yamma domin taimakawa gwamnatoci da jama'a na yankin yaki da cutar Ebola.
Dujarric ya ce, wani jirgin ruwa makare da shinkafa kimanin tan dubu 7 ya isa birnin Freetown na kasar Saliyo daga Cotonou dake kasar Benin, za dai a saukar da wasu kayayyakin abinci a Freetown, kafin jirgin ya kara gaba zuwa Monrovia dake kasar Liberia.
A kuma daidai wannan lokacin ne shugaban tawagar MDD a kan daukar mataki na gaggawa a kan cutar Ebola, Anthony Banbury ya isa kasar Guinea a jiya Talata, kuma ana sa rai zai gana da hukumomin kasar, ciki har da shugaban kasar ta Guinea, a game da matakan da za'a dauka na ci gaba a game da dakile cutar Ebola, shugaban zai kuma yiwa 'yan kasar ta Guinea jawabi a game da tsarin gudanar da ayyuka wanda majalisar dinkin duniyar ta tsara a kokarin da take yi na dakile cutar Ebola.
Hukumar lafiya ta duniya WHO ita kuma tuni ta yabawa taimakon da kasar Canada ta yi na samar da allurar rigakafin cutar ta Ebola wadda za'a gwada ta a jikin 'dan adam. (Suwaiba)