A yau Litinin ne hukumar lafiya ta duniya WHO ta ayyana kasar Najeriya a matsayin kasar da ta yi nasarar kawar da cutar Ebola kwata-kwata a kasar bayan da aka tabbatar da cewa, babu ko da mutum guda da ke dauke da cutar a cikin kwanaki 42 da suka gabata.
Wakilin hukumar lafiya ta duniya da ke Najeriya Rui Dama Gaz ne ya da ba wannan sanarwa a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.
Kakakin ma'aikatar lafiya ta Najeriya Dan Nwomeh ya shaida wa wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin ta gajeren sakon wayar salula cewa, Najeriya ta yi maraba da wannan ci-gaba da aka samu.(Ibrahim)