Hukumomin kiwon lafiya na kasar Guinee sun samu taimakon safar hannu kusan miliyan 5,6 daga bankin duniya, domin taimakawa ma'aikatan kiwon lafiya na kasar da annobar cutar Ebola ta fi shafa wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, tare da mutuwar ma'aikatan kiwon lafiya 35 daga cikin 76 da aka gano suna dauke da cutar tun lokacin barkewar wannan annoba.
Ko da yake matsalar ta fara kyautatuwa a bangaren ma'aikatan lafiya, kamar yadda babban shugaban yaki da cutar Ebola ya sanar a ranar Asabar 18 ga wata, tare da bayyana cewa, har yanzu kuma ba'a samu wasu ma'aikatan kiwon lafiya ba da suka kamu tun yau da sati. Amma kuma yana da muhimmanci da a karfafa matakan yin rigakafi da na kariya a wajen ma'aikatan kiwon lafiya.
Wadannan safunan hannu da bankin duniya ya ba da za'a isar da su zuwa hukumomin kiwon lafiya daban daban na kasar. A yanzu haka ma wasu asibitocin babban birnin kasar sun fara aiki da su, in ji hukumomin kasar Guinee. (Maman Ada)