Wata tawagar kiwon lafiya ta kasar Rwanda za ta shiga gamayyar gabashin Afrika (CEA) da kasar Rwanda ke ciki, domin shiga yaki da cutar Ebola a yammacin nahiyar Afrika.
Wannan tawaga za ta kunshe likitoci 41 da wasu ma'aikatan lafiya 578 da suka fito daga kasashe mambobi biyar na kungiyar CEA, in ji wata sanarwar ma'aikatar kiwon lafiyar kasar Rwanda a ranar Jumma'a.
Wannan ma'aikata na ganin cewa, rashin matakan kariya da suka dace da kuma rashin ilimin kiwon lafiya da rashin aiwatar da wasu matakan killace maras lafiya suka kara tsananta yaduwar annobar Ebola a yammacin nahiyar Afrika.
Kasar Rwanda ta bukaci al'ummarta da su kaucewa yin tafiyar da ba ta dole ba zuwa kasashen Liberiya, Guinee da Saliyo. (Maman Ada)