in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi kiran da a kara samar da tallafin ma'aikatan lafiya don yaki da cutar Ebola
2014-10-17 10:05:11 cri

Kungiyar tarayyyar kasashen Afirka ta AU ta yi kira ga kasashe mambobin kungiyar da abokan huldarta da su kara samar da tallafin ma'aikatan lafiya a yakin da take da cutar Ebola a yammacin Afirka.

Shugabar hukumar zartarwar kungiyar Madam Nkosazana Dlamini-Zuma ce ta bayyana hakan a ranar Alhamis a hedkwatar kungiyar da ke birnin Addis Ababa na kasar Habasha, inda ta ce, karancin muhimman kayayyakin more rayuwa da ma'aikatan lafiya na daga cikin manyan kalubalen da ke addabar kungiyar a kokarin da take na yaki da wannan annoba.

Kungiyar ta AU ta ce, cutar ta Ebola ta fi kamari ne a kasashen Liberia, Saliyo da kuma Guinea, don haka akwai bukatar a kara samar da ma'aikatan lafiya a wadannan kasashe don ganin an kawar da wannan cuta.

Shugabar kungiyar ta kuma bukaci kasashe mambobin kungiyar da kowanensu ya taimaka da ma'aikatan sa-kai kimanin 10 zuwa 20, baya ga wasu kasashe da kungiyar take tattaunawa da su don ganin su ma sun agaza da ma'aikatan lafiya.

Ya zuwa yanzu dai kungiyar ta AU ta riga ta tura ma'aikatan sa-kai zuwa kasashen Liberia da Saliyo a kokarin da take na yaki da cutar ta Ebola. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China