in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO ta jaddada muhimmancin taimaka wa kasashen Afirka wajen tinkarar cutar Ebola
2014-10-17 16:46:41 cri
Wata jami'ar hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayyana a jiya Alhamis 16 ga wata, cewar yanzu hukumar na sa ido sosai kan kasashen Afirka 15, a kokarin magance yaduwar cutar Ebola mai saurin kisa a wadannan kasashen da ba su da ingantattun kayayyakin kiwon lafiya, sa'an nan ba su da karfi wajen shawo kan cututtuka.

A yayin taron manema labarai da aka shirya a fadar Palace of Nations da ke Geneva, Isabelle Nuttall, shugabar sashen yin gargadi da tinkarar matsaloli na hukumar WHO ta furta cewa, duk da cewa, an gano wasu mutanen da suka kamu da cutar Ebola a kasashen Amurka da Jamus da kuma Spain, amma wadannan kasashe suna da karfi wajen shawo kan yaduwar cutar. Amma kasashen da ke makwabtaka da kasashen Liberia, Saliyo da kuma Guinea ba su da kayayyakin jiyya masu inganci,wannan ya sa WHO ke nuna damuwa ganin yadda cutar Ebola za ta iya yaduwa a kasashen, wanda hakan zai kawo babbar illa.

Haka zakila, Madam Nuttall ta ce, hukumar WHO za ta inganta hadin gwiwa tare da kasashen Afirka 15 da ke jawo hankalinta, a kokarin ba su tabbaci wajen samun kayayyaki da fasahohin rigakafin cutar Ebola. A sa'i daya kuma, tana fatan wadannan kasashe za su dauki matakan da suka dace sosai a dukkan fannoni.

A wannan rana kuma, shugabar hukumar zartarwar kungiyar tarayyar Afirka AU Madam Nkosazana Dlamini-Zuma ta yi kira ga kasashe mambobin AU da sauran kasashen duniya da su duba yiyuwar kara tura masu aikin jiyya zuwa kasashe masu fama da cutar Ebola. Kawo yanzu dai, a cewar Madam Zuma, AU na da masu aikin sa kai kimanin 100 ne, don haka tana bunkatar kowace mambar kungiyar da ta ba da gudummawar a kalla masu aikin sa kai 10 zuwa 20.

Bugu da kari, a wannan rana, kungiyar tarayyar Turai EU ta kira babban taro na kwanaki uku kan yadda za a tinkari cutar Ebola, inda ta yi kira ga mambobinta da su inganta hadin kan da ke tsakaninsu, da kyautata kwarewarsu wajen sanya ido, da kuma kara sanya na'urorin binciken cututtuka a filayen jiragen sama, domin tinkarar matsalar yaduwar cutar Ebola.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China