Shugabar kasar Liberiya Ellen Johnson Sirleaf ta yi kira a ranar Lahadi ga gamayyar kasa da kasa da ta tallafawa kasarta a wajen yakin da take da cutar Ebola. Wannan yaki ne da a cikinsa kowa na da nasa matsayi. Wannan cuta ba ta san iyaka ba, kuma tana janyo barna a yammacin Afrika, ta kasance a fannin kiwon lafiyar jama'a, tattalin arziki ko kuma a cikin al'ummomi, wannan matsala tuni labarinta ya kai dukkan shiyyar, da ma duniya baki daya, in ji madam Sirleaf a cikin wata budaddar wasika.
Shugabar Liberiya ta yi kashedin cewa, cutar Ebola na cigaba da bazuwa cikin kasashe uku masu karamin karfi wato Liberiya, Saliyo da Guinea, tare da nuna cewa, nauyin kowa ne na aike da sako: Ba za'a barin miliyoyin 'yan yammacin Afrika ba, su kadai da wannan abokin gaba da ba su san shi ba, da kuma ba su karfin kare kansu a gabansa. (Maman Ada)