Wani matashin da ya fito daga kasar Guinee zuwa birnin Dakar ya samu kamuwa da cutar Ebola. A dunkule, an gano mutane 74 da suka yi mu'amala da mara lafiya, amma gwaje gwaje sun tabbatar da cewa ba su dauke da cutar Ebola, in ji kungiyar WHO.
Majalisar dinkin duniya ta yaba wa hukumomin kasar Senegal da suka samu nasarar kebance mutum guda da aka gano da cutar Ebola a cikin wannan kasa.
Mutumin kuma ya samu lafiya, kana ya koma kasar Guinee a tsakiyar wata Satumba. Kasar ta Senegal ta rike matakin shirin ko ta kwana a tsawon kwanaki arba'in da biyu, kuma sau biyu na lokacin bayyanar cutar da alamun cutar na farko na kwanaki ashirin da daya, domin gano cikin gaggawa wasu sabbin wadanda suka kamu da cutar a cikin kasar. (Maman Ada)