in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta sha alwashin tsayawa da Afrika wajen yaki da cutar Ebola
2014-09-26 09:45:14 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a ranar Alhamis din nan 25 ga wata ya ce, al'ummar Sinawa za su kasance masu tsayawa tare da al'ummar Afrika a ko da yaushe wajen yaki da cutar Ebola.

Mr. Wang ya fadi hakan ne a lokacin da yake jawabi a babban taro kan matakin da za'a dauka wajen yaki da cutar Ebola wanda aka yi lokacin zaman mahawaran MDD.

Ya ce, annobar ba ta da imani, amma al'umma za su taimaki junansu cikin kauna, don haka kasar Sin ta riga ta samar da magunguna na ba da kariya nan take, kayayyakin aiki a asibiti, da sauran abubuwan da ake bukata na ba da kariya ga kasashen Guinea, Liberiya, Guinea-Bissau da Saliyo.

Yanzu haka, ya yi bayanin cewa, kasar Sin ta riga ta aike da ma'aikatan lafiya fiye da 170 zuwa kasashen da wannan annoba ta yi kamari, suna nan kuma suna aiki ba dare ba rana domin taimakawa al'umman wannan wuri da annobar ta yi kamari.

Ministan harkokin wajen na Sin har ila yau ya jaddada cewa, domin ba da taimako ga bukatun wadannan kasashe da cutar ta yi kamari, kasar Sin za ta ci gaba da kara wassu kayayyakin bukata ta hanyar tura manyan jami'an kiwon lafiya zuwa kasashen domin musanyar ra'ayi a kan yadda za'a murkushe wannan annoba, za ta kuma yi aiki tare da sauran al'ummomin kasashen waje domin ba da horo ga jami'an kiwon lafiya domin zuwa wadannan kasashe da annobar ta yi kamari, sannan ta taimaka wajen kafa cibiyoyin ba da magani. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China