Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya sanar da kudurinsa na kiran babban taro na shugabannin kasashen duniya a lokacin da za'a yi babban taron majalissar na shekara shekara domin tattauna yadda za'a hana yaduwar cutar Ebola.
Kamar yadda kakakin majalissar ya sanar a ranar Talatan nan 23 ga wata, wannan babban taron a kan Ebola da za'a kira dangane da barkewar cutar, za'a yi shi ne a safiyar ranar Alhamis din nan mai zuwa 25 ga wata a cibiyar majalissar dake birnin New York.
Mahalarta wannan taro za su hada da shugaban kasar Guinea Alpha Conde, shugaban kasar Liberiya Madam Ellen Johnson Sirleaf, da kuma shugaban kasar Saliyo Ernest Bai Koroma wadanda za su yi bayani da wayar sadarwa kai tsaye daga kasashensu.
Taron har ila yau zai fitar da sanarwar daga wakilan mambobin majalissar da kuma sauran manyan hukumomi masu cin gashin kansu kamar su hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, kwamitin tarayyar kasashen Afrika AU, kwamitin tarayyar kasashen Turai EU, babban bankin duniya da kungiyar ba da gaji ta duniya Red Cross. (Fatimah)