in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An nada sabon shugaban tawagar MDD game da yaki da cutar Ebola
2014-09-24 10:47:56 cri

Babban sakatare na MDD, Ban Ki-moon, ya sanar a ranar Talata da nada David Nabarro na kasar Ingila, a matsayin manzon musamman domin yaki da cutar Ebola, kana Anthony Banbury, 'dan kasar Amurka, a mukamin wakilin musamman kuma shugaban tawagar MDD game da yaki da cutar Ebola.

An dauki matakin ne bayan shawarwari tare da shugabar kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO), madam Margaret Chan, in ji kakakin mista Ban Ki-moon. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China