in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF zai samar wa kasashen uku dake fama da cutar Ebola taimakon kudi dallar Amurka miliyan 130
2014-09-27 17:17:56 cri
Jiya Jumma'a 26 ga wata, a yayin taron daraktan zartaswa na asusun ba da lamuni na IMF, an zartas da samar wa kasashen uku da suka fi fama da yaduwar cutar Ebola a yammacin nahiyar Afirka taimakon kudi dallar Amurka miliyan 130.

Cikin wata sanarwar da IMF ya samar a wannan rana, an ce, kasar Guinea za ta samu dallar Amurka miliyan 41, kasar Liberiya za ta samu dallar Amurka miliyan 49, yayin da kasar Saliyo za ta samu dallar Amurka miliyan 40. Kuma bisa hasashen da IMF ya yi, an ce, gaba daya yawan bukatun kudadensu wajen yaki da cutar Ebola ya kai dallar Amurka miliyan dari uku.

Haka kuma, shugabar IMF Christine Lagarde ta bayyana cewa, cutar Ebola ta haifar da babbar illa ga wadannan kasashen uku, suna bukatar taimakon gamayyar kasa da kasa matuka a halin yanzu.

Mataimakiyar babbar darektar hukumar kiwon lafiyar kasa da kasa ta WHO Marie Paule Gini ta bayyana a ran 26 ga wata cewa, a halin yanzu, hukumar WHO da bangarorin da abin ya shafa na dukufa wajen binciken allurar rigakafi kan cutar, mai iyuwa ne za a iya fara yin amfani da allurar a watan Janairu a shekara mai zuwa a wasu yankuna. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China