Ya zuwa yanzu, MDD ta gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya a nahiyar Afirka guda 9, inda kasar Sin ta halarci 7 daga cikinsu, dangane da lamarin, Hua Chunying ta bayyana cewa, kasar Sin ta kara tura sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa kasar Sudan ta Kudu, wannan wani muhimmin mataki ne da Sin ta dauka wajen goyi bayan MDD kan aikinta na kiyaye zaman lafiya. Haka kuma, kasar Sin za ta ci gaba da halartar aikin kiyaye zaman lafiya da MDD take gudanarwa don ba da gudummawa kan kiyaye zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, musamman ma a nahiyar Afirka. (Maryam)