Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin madam Hua Chunying, ta bayyana hakan a yayin taron manema labaru a ranar Jumma'a.
Inda ta bayyana cewa, kasar Sin tana son kara shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya a kasar Sudan ta Kudu bisa bukatar MDD.
Har ila yau, jami'ar ta bayyana cewa, an samu ci gaba a wasu fannoni kan yanayin da kasar Sudan ta Kudu ke ciki. Kasar Sin ta lura da cewa, shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir, da shugaban dakarun adawa Meshal sun tattauna kai tsaye, tare da daddale yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kwanan baya, kasar Sin ta maraba sosai kan wannan, ta kuma nuna yabo sosai ga sassa daban daban da abin ya shafa, ciki har da kungiyar IGAD da su kokarta wajen kyautata shawarwarin tsagaita bude wuta tsakanin bangarori daban daban na kasar. Tana kuma fatan matakan da suka dauka za su amfanawa kara sassauta yanayin da kasar ke ciki.
Har kullum kasar Sin na sa himma wajen shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya bisa tsarin MDD, tana son taka rawarta wajen inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar Afrika. Akwai ma'aikatan kasar Sin 360 da a yanzu haka suke gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya a kasar Sudan ta Kudu. Idan akwai bukatar ma, kasar Sin tana son kara shiga irin ayyuka bisa rokon MDD in ji madam Hua Chunying. (Bilkisu)