Kudurin ya bukaci kasashen Sudan da Sudan ta Kudu da su kafa hukumar gudanar da harkokin shiyyar Abyei da majalisar dokokin shiyyar cikin sauri. Kuma ya kamata a kafa ofishin 'yan sanda a shiyyar don tabbatar da tsaron lafiyar shiryyar ciki har da na muhimman ayyukan hakar man fetur. Kana kwamitin sulhu ya jaddada cewa, baya ga sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD dake shiyyar da ofishin 'yan sanda na wurin, bai kamata a jibge sojoji da dakaru a wannan shiyya ba.
Hakazalika kuma, kwamitin sulhu ya bayyana cewa, zai yi bincike kan ka'idojin sojojin kiyaye zaman lafiya dake shiyyar Abyei, da sake daidaita sojojin bisa yadda kasashen Sudan da Sudan ta Kudu suka yi alkawarin janye sojoji daga yankin iyakar kasa. (Zainab)