Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu kuma mataimakin shugaban jami'iyyar SPLM James Wani Igga yau Talata 1 ga watan Yuli a nan birnin Beijing.
A yayin ganawar, Li Keqiang ya ce, kasar Sin ta yaba wa kokarin da gwamnatin Sudan ta Kudu take yi wajen warware rikicin kasar cikin ruwan sanyi da kuma shiga tsakani da kungiyar hadin kan gwamnatocin kasashen Gabashin Afirka wato IGAD take yi. Kasar Sin na fatan za a samu sulhuntawar al'umma da maido da tsaro da kuma kwanciyar hankali a Sudan ta Kudu cikin hanzari. Kasar Sin kuma na son ci gaba da taka rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwa a kasashen Sudan da Sudan ta Kudu.
A nasa bangaren, mista Wani ya ce, kasarsa ta gode wa gwamnatin Sin da ta mara mata baya wajen samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma bunkasuwar tattalin arziki. Tsarin yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka da mista Li Keqiang ya gabatar yayin da yake ziyara a Afirka a kwanan baya ya karfafa gwiwar Kasashen Gabashin Afirka sosai, don haka suna son hada kai da kasar Sin wajen shimfida hanyoyin dogo da tsarin zirgar-zirga a yankin. Haka kuma Sudan ta Kudu za ta ci gaba da himmantuwa wajen tabbatar da samun zaman lafiya da sulhuntawa, da kuma tabbatar da tsaron lafiyar ma'aikata da kamfanonin kasar Sin a kasar.
A wannan rana kuma, mataimakin shugaban kasar Sin Li Yuanchao shi ma ya gana da mista Wani. (Tasallah)