A yau Laraba yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing, Hong Lei, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya yi karin bayani kan yadda kasar Sin za ta tura sojojinta shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya da MDD ke gudanarwa a kasar Sudan ta Kudu.
An yi tambayar cewa, wani jami'in MDD mai kula da harkokin kiyaye zaman lafiya ya ce, wannan ne karo na farko da kasar Sin za ta tura sojoji 850 shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya da MDD ke gudanarwa a Sudan ta Kudu. Wane karin bayani Sin za ta yi kan lamarin?
Hong Lei ya ce, har kullum kasar Sin na shiga ayyukan MDD a fannin kiyaye zaman lafiya cikin himma da kwazo. A cikin dukkan kasashen da ke da kujerar dindindin a kwamitin sulhu na MDD, kasar Sin ta fi tura yawan sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa ketare. Yanzu 'yan sandan kasar Sin suna aikin kare zaman lafiya a kasar Sudan ta Kudu. Da zummar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar Afirka, da samar da kyakkyawan sharadi wajen raya Sudan ta Kudu, da kuma sauke nauyin da aka dora wa kasar Sin yadda ya kamata, kasar Sin na son kara ba da gudummowa wajen daidaita batun Sudan ta Kudu yadda ya kamata da kuma kwantar da kura a wannan kasa. (Tasallah)