in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon yana maraba da kudurin kwamitin sulhu game da batun Sudan ta Kudu
2014-05-28 15:50:54 cri
Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayar da wata sanarwa ta hanyar kakakinsa, inda ya nuna maraba da kudurin kwamitin sulhu na MDD game da gyara ayyukan tawagar musamman ta MDD dake kasar Sudan ta Kudu, kana ya kalubalanci bangarori daban daban na kasar da su yi hadin gwiwa tare da tawagar musamman don aiwatar da ayyukanta yadda ya kamata.

Sanarwar ta jaddada muhimmancin sabbin ayyukan tawagar musamman ga kasar Sudan ta Kudu a fannin neman zaman lafiya da tsaro, kana sanarwar ta bukaci kasashen da suke yunkurin tura sojoji zuwa kasar da su tura sojoji, 'yan sanda su koma samar da kyawawan sharuda ga kasar.

Ban da wannan kuma, sanarwar ta ce, Ban Ki-moon ya yi kashedi ga bangarori daban daban dake kasar Sudan ta Kudun da su dauki nauyin tabbatar da tsaron jama'ar kasar da yanke hukunci ga wadanda suka aikata laifuka, kazalika sanarwar ta kalubalanci bangarorin da suke dauki-ba-dadi da juna da su aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka daddale a watan Janairu da na Mayun bana cikin hanzari, daga nan sai ya yi fatan ingiza yunkurin siyasa, da kuma samar da hadin gwiwa ga tawagar musamman ta MDD don aiwatar da ayyukansu yadda ya kamata. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China