in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin zai halarci babban taron MDD karo na 69
2014-09-22 20:14:13 cri
A yayin taron maneman labarai da aka saba yi a yau Litinin 22 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi zai halarci babban taron MDD karo na 69, haka kuma, zai kai ziyarar aiki a kasashen Mexico da Amurka.

Madam Hua ta ce, za a bude babban taron MDD karo na 69 a hedkwatar MDD dake birnin New York a ran 16 ga watan Satumba, kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi zai halarci taron tare da tawagar kasar Sin tun ranar 24 zuwa 28 ga wata, zai kuma yi jawabi game da manufofin kasar Sin dangane da harkokin zaman lafiya, neman ci gaba, da yin hadin gwiwa, bugu da kari, jawabinsa zai shafi matsayi da ka'idojin kasar Sin kan muhimman harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China