Yau Litinin 8 ga wata, a birnin Geneva, Zeid Ra'ad Zeid Al-Hussein, sabon babban kwamishinan kula da kare hakkokin dan Adam na MDD ya yi kira ga kasashen duniya da su mai da hankali kan halin da ake ciki a yankunan Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka, da yadda ake kiyaye hakkokin dan Adam a wurin.
A yayin taro karo na 27 da kwamitin kula da kare hakkokin dan Adam na MDD ya bude a wannan rana, Al-Hussein ya nanata cewa, mai yiwuwa ne duk wanda ya kai hare-hare kan fararen hula na ko wace kabila bisa duk wani dalilin siyasa da addini, hakan na iya take hakkin Bil'Adama, kumatilas ne a hukunta shi. Bisa tanade-tanaden da ke cikin dokokin kasa da kasa, ya zama wajibi kasashen duniya da kungiyoyi masu dauke da makamai su dauki wajababbun matakai, su yi namijin kokarin sassauta illar da aikace-aikacen nuna karfin tuwo suka haddasa kan fararen hula, sa'an nan, wajibi ne su tabbatar da tsaron lafiyar fararen hula yayin da suke daukar matakan soja. (Tasallah)